Litinin 3 Agusta 2026 - 22:34
An Bayyana Falalar Musamman ta Ziyarar Sayyidush Shuhada (A.S.) a Cikin Ruwayoyi: Waɗanda Ba Su Samu Zuwa Arba’in Ba Kada Su Manta da Ziyara Daga Nesa

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Ali Husaini, malami kuma mai bincike a Hauzar Ilimi ta Qum, ya bayyana cewa ya dace masu ziyara su gudanar da wannan tafiya mai albarka cikin sani, ikhlasi da kyakkyawar niyya, musamman da niyyar wakiltar dukkan shahidai, musamman Shahidin jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da shahidan yaƙin da aka tilasta wa Iran, domin su samu albarkar ruhaniya da ke tattare da wannan ziyara.

Da yake magana da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza game da matsayin littafin “Kamiluz Ziyarat” wajen bayyana falalolin ziyartar Ahlul Baiti (A.S.), Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Ali Husaini ya ce: "Littafin “Kamiluz Ziyarat” yana daga cikin ingantattun littattafan hadisi na Shi’a kan batun ziyara. Littafin ya ƙunshi kusan ruwayoyi 750, daga cikinsu kusan 500 sun shafi falala, ladubba, lada da ziyarorin Imam Husaini (A.S.)."

Ya bayyana cewa an fassara wannan littafi mai daraja zuwa harshen Farisanci da wasu harsuna daban-daban na duniya, kuma malamai da masu bincike sun kasance suna ba shi muhimmiyar kulawa.

Da yake ishara zuwa wata ruwaya da ke cikin littafin, ya ƙara da cewa a babi na 44 na “Kamiluz Ziyarat”, an kawo wata ruwaya da ke magana kan matsayin mutanen da ba su samu damar zuwa Karbala mai tsarki da kansu ba, amma suka samar da hanya da abubuwan da ake buƙata domin wasu su je ziyara.

Taken babin shi ne: “ثواب من زار الحسین علیه‌السلام بنفسه أو جهز إلیه غیره”, wato ladan wanda ya ziyarci Imam Husaini (A.S.) da kansa ko kuma ya tanadar wa wani damar zuwa ziyara.

Ladan hidimar masu ziyarar Imam Husaini (A.S.) kamar girman Dutsen Uhud

Hujjatul Islam wal Muslimin Husaini ya ci gaba da cewa a cikin wannan ruwaya, mai ruwayar ya tambayi Imam Sadik (A.S.) game da ladan waɗanda suke samar da kuɗi ko kayan aikin da wasu za su yi amfani da su wajen ziyara.

Sai Imam Sadik (A.S.) ya amsa da cewa:

«یُعْطِیهِ اللَّهُ بِکُلِّ دِرْهَمٍ أَنْفَقَهُ مِثْلَ أُحُدٍ مِنَ الْحَسَنَاتِ وَ یُخْلِفُ عَلَیْهِ أَضْعَافَ مَا أَنْفَقَهُ»

“Allah zai ba shi saboda kowane dirhami da ya kashe, ladan da ya kai girman Dutsen Uhud na kyawawan ayyuka, sannan Ya mayar masa da ninkin abin da ya kashe.”

Ya bayyana cewa wannan ruwaya tana nuna irin girman darajar hidima ga masu ziyarar Imam Husaini (A.S.) da kuma samar musu da abubuwan da suke buƙata domin gudanar da ziyara, domin hakan yana daga cikin ayyuka masu matuƙar daraja kuma masu yawan lada a wurin Allah Maɗaukakin Sarki.

Da mutane sun san falalar ziyara, da sun mutu saboda tsananin ɗoki

Wannan malamin Hauza ya nakalto wata ruwaya daga Imam Muhammad Baƙir (A.S.), inda ya ce Imam Baƙir (A.S.) ya bayyana:

«لَوْ یَعْلَمُ النَّاسُ مَا فِی زِیَارَةِ قَبْرِ الْحُسَیْنِ(ع) مِنَ الْفَضْلِ لَمَاتُوا شَوْقًا وَ تَقَطَّعَتْ أَنْفُسُهُمْ عَلَیْهِ حَسَرَاتٍ»

“Da mutane sun san falalar da ke cikin ziyartar kabarin Husaini (A.S.), da sun mutu saboda tsananin ɗoki, kuma rayukansu sun yanke saboda tsananin nadamar rashin yin wannan ziyara.”

Ya ƙara da cewa a ci gaban wannan ruwaya, Imam Baƙir (A.S.) ya bayyana cewa duk wanda ya je ziyarar Sayyidush Shuhada (A.S.) cikin ƙauna, sani da ɗoki, Allah zai rubuta masa ladan Hajji dubu da aka karɓa, Umra dubu da aka karɓa, da kuma ladan shahidai dubu daga cikin shahidan yaƙin Badar.

Hujjatul Islam wal Muslimin Husaini ya jaddada cewa waɗannan ruwayoyi suna bayyana girman falalar ruhaniya da ke tattare da ziyarar Imam Husaini (A.S.), da kuma muhimmiyar rawar da ziyara take takawa wajen ƙarfafa alaƙar zuciyar muminai da juyin Ashura.

Saboda haka, a kowace shekara miliyoyin masoya Ahlul Baiti (A.S.) kan fuskanci wahalhalu daban-daban domin isa Karbala mai tsarki a gab da Arba’in, don sake sabunta mubaya’arsu ga manufofin Sayyidush Shuhada (A.S.).

Mai ziyartar Imam Husaini (A.S.) ya ziyarci Manzon Allah (S.A.W.A.)

Ya ci gaba da nakalto wata ruwaya daga Imam Sadik (A.S.) da ke cikin littafin “Kamiluz Ziyarat”, inda ya ce Imam Sadik (A.S.) ya bayyana:

«إِنَّ زَائِرَ الْحُسَیْنِ بْنِ عَلِیٍّ(ع) زَائِرُ رَسُولِ اللَّهِ(ص)»

“Lallai maziyarcin Husaini ɗan Ali (A.S.) maziyarcin Manzon Allah (S.A.W.A.) ne.”

Wannan malamin Hauza ya ƙara da cewa wannan hadisi yana bayyana babban matsayi da Imam Husaini (A.S.) yake da shi a wurin Allah Maɗaukakin Sarki da kuma ManzonSa Mai Girma (S.A.W.A.). Haka kuma yana nuna cewa ziyartar Imam Husaini (A.S.) wata hanya ce ta neman kusanci zuwa ga Allah, ManzonSa (S.A.W.A.) da kuma Ahlul Baiti (A.S.).

Wadanda ba su samu zuwa Karbala Arba’in ba kada su manta da ziyara daga nesa

Hujjatul Islam wal Muslimin Husaini, yayin da yake magana kan zuwan kwanakin Arba’in din Imam Husaini (A.S.), ya jaddada cewa ya dace masu ziyara su halarci wannan tafiya mai albarka cikin sani, ikhlasi da kyakkyawar niyya, musamman da niyyar wakiltar dukkan shahidai, musamman Shahidin jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da shahidan yaƙin da aka tilasta wa Iran (da sauran shuhada musamman na Harkar Musulunci), domin su amfana da albarkokin ruhaniya da ke tattare da wannan tafiya.

Wannan mai bincike a fannin Hauza ya kuma yi magana ga waɗanda ba su da damar halartar Karbala mai tsarki, inda ya ce: "Waɗanda ba su samu zuwa Arba’in ba za su iya zuwa masallatai, wuraren ibada masu tsarki (kamar Husainiyoyi) da kuma haraman zuriyar Annabi (A.S.), su karanta Ziyarar Ashura, su yi addu’a, su nemi taimakon Allah ta hanyar tawassuli ga Hazrat Waliyyul Asr (A.F.), sannan su aika gaisuwa ga Sayyidush Shuhada (A.S.) daga nesa, domin su samu rabonsu daga albarkokin ruhaniya na waɗannan kwanaki.

A ƙarshe, ya yi ishara da wata ruwaya daga Husaini ɗan Thuwair, wadda ya ruwaito daga Imam Ja’afar Sadik (A.S.), inda ya ce: Ni tare da Yunus ɗan Zabyan, Mufaddal ɗan Umar da Abu Salama mun kasance a wajen Imam Sadik (A.S.). Yunus, wanda shi ne mafi girma a cikinmu, ya ce: “Raina fansarka, na kan yawaita tunawa da Husaini ɗan Ali (A.S.); idan hakan ya faru, me zan faɗa?”

Sai Imam Sadik (A.S.) ya ce masa: “Ka faɗi sau uku: ‘Sallallahu alaika ya Aba Abdillah’, domin lallai gaisuwar tana isa ga Imam Husaini (A.S.) daga nesa da kuma kusa.”

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha